Iraki: Bam ya kashe mutane a bikin Aure
March 9, 2017Talla
Likitoci da ke karban jinya sun ce akwai mutane 25 da ke fama da munanan raunuka, sai dai kawo yanzu babu wadanda suka dau alhakin kai harin, amma hukomi a kasar sun ce kungiyar IS ta sha kai hare-hare makamancin wannan a kan fararen hula da ma jami'an tsaro.
A yanzu dai dakarun gwamnatin Iraki na fafatawa a yammacin birnin Mosul na ganin sun karbe iko na sauran yankunan da ke karkashin ikon kungiyar ta IS, inda wasu rahotanni ke cewa tuni jagoran kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi ya tsere daga birnin.