Sistani ya magantu a kan rikicin Iraki
November 22, 2019Talla
A lokacin da yake hudubar sallar Jumma'a, jagoran musulmi na mabiya mazhabar Shi'a, Ayatollah Ali al-Sistani ya bukaci jam'iyyun siyasa su gaggauta amincewa da dokokin sauyin tsarin mulki kuma su saurari bukatun masu zanga-zanga, domin kawo karshen rikici a kasar. A yanzu dai masu zanga-zangar na rike da bangare guda na manyan gadoji uku da ke Bagadaza babban birnin kasar wadanda kuma ke zaman hanyar isa fadar gwamnati, duk kuwa da cewar gwamnatin ta jibge jamai'an tsaro domin dakile zanga-zangar .
Tuni Majalisar Dinkin Duniya tare da kasashen Turai suka yi Allah wadai da amfani da karfin da jami'an tsaro ke yi a kokarin dakile masu zanga-zangar.