1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki: Kokarin kwace birnin Mosul daga IS

October 17, 2016

Dakarun Iraki na ci gaba da fafatawa domin sake kwace birnin Mosul daga hannun 'yan kungiyar IS, inda a karon farko sojojin gwamnati ke hadaka da kungiyoyin sa-kai da a baya basa jituwa.

Barin wuta domin kwace birnin Mosul daga IS
Barin wuta domin kwace birnin Mosul daga ISHoto: picture-alliance/abaca/Y. Keles

Gwamnatin Iraki ta kwashe kwanaki tana kai kayan yaki da shirya dakaru domin sake kwace birnin na Mosul da 'yan kungiyar IS masu ikirarin neman kafa daular Islama suka karbe shekaru biyu da suka gabata. Kuma da sanyin safiyar wannan Litinin Firaminista Haider al-Abadi ya bayyana kaddamar da farmakin na sake kwato birnin na Mosul inda yake cewa.

"Dakaru za su sake kwato Mosul, burin da suka saka a gaba shi ne fatattakar 'yan kungiyar IS daga Mosul domin 'yanta mutane. Kuma da ikon Allah za mu samu nasara."

Wannan jawabi na Firaminista ya zo a lokacin da hayaki ke turnike yankin birnin Mosul sakamakon farmakin sojoji. Saud Masoud na daya daga cikin rundinoni na musamman na sojojin Iraki ya nunar da yadda suka aiki tare da mayakan Peshmega.

Firaministan Iraki Haider al-AbadiHoto: picture-alliance/dpa/R. Jensen

"Dakarun Pesh-mega za su rike yankin da suke bukata na Goj-galli. Daga wannan gari na Goj-galli mu kuma za mu nausa Mosul."

 

Hada hannu waje guda domin samun nasara

 

Wani abu kuma shi ne yadda mayakan sa-kai daga bangori daban-daban za su ci gaba da dangantaka ganin ba kasafai suke shiri da juna ba, amma yanzu sun dunkule domin yaki da mayakan IS saboda sake kwato birnin Mosul da ke zama birnin na biyu mafi girma a kasar ta Iraki. Manjo Shwan Ihsan na cikin rundunar Kurdawa yana nuna kwarin gwiwa kan yaki da 'yan kungiyar IS.

"Muna rike da yankunan nan da ke wajen birnin. Wannan shi ne farkon samamen da aka kaddamar domin kwace Mosul. Muna da kwarin gwiwa. Mun yi nasarar mayar da martani kan 'yan IS lokacin da suke da karfi, kuma yanzu suna da rauni. Su ba komai ba ne."

Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip ErdoganHoto: Reuters/M. Sezer

Tuni Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiya wanda dakarun kasarsa suke cikin Iraki kuma ake samun takun-saka kan batun, yake cewa tilas Turkiya ta kare manufofinta kan iyaka da kasashen Iraki da Siriya da ake samun tashe-tashen hankula.

 

Samame domin kwace Mosul

 

"Yanzu an fara samamen sake kwace Mosul. Wannan samame zai ci gaba. Me suke cewa? Turkiya kar ta shiga Mosul. Yanzu me zan yi? Muna da iyaka mai nisan kilomita 350 da Iraki kuma muna karkashin barazana. Turkiya tana da iyaka mai nisan kilomita 911 da Siriya kana nisan kilomita 350 da Iraki."

Wannan farmaki na sake kwace Mosul na zama samamen sojoji mafi girma da aka kaddamar a Iraki tun bayan janyewar dakarun Amirka daga kasar a shekara ta 2011, kuma idan aka samu nasara haka na zama babban koma-baya ga tsagerun kungiyar IS masu ikirarin neman kafa daular Islama.