Iraki: Kurdawa na zaben neman ballewa
September 25, 2017Talla
Kawo yanzu dai wannan zabe na ci gaba da haifar da fargabar ga makomar zaman lafiya a yankunan da suka sha fama da masu tada kayar bayan kungiyar IS. A nasu bangaren gwamnatin Turkiyya, ta dauki matakan soji na toshe kan iyakar ta da yankunan Kurdawan a yunkurin nuna rashin goyon bayan zaben neman ballewar. Wannan ya sa Firaiminstan Iraki Haider al-Abadi, ya yi kakkausar suka ga matakin Kurdawan na neman raba kasa.
"Ba za mu yi watsi da al'ummar Kuradawa ba, mun yi watsi da shirin samar da yanki mai wariya. Iraki za ta ci gaba da kasancewa ta al'ummar Iraki, ba za mu amincewa kowa ya taka doka ba."