1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki: Pasinjojin jirgin sama sun ketara rijiya da baibai

Gazali Abdou Tasawa
July 26, 2018

A Iraki wasu fasinjojin jirgin sama 157 da ke balaguro a wani jirgin kamfanin Iraki Airways sun ketara rijiya da baibai bayan da fada ya kaure a sararin samaniya tsakanin direban jirgin da mataimakinsa ana cikin tafiya.

Iraq Iraqi Airways
Hoto: AP

A kasar Iraki wasu fasinjojin jirgin sama 157 da ke balaguro a cikin wani jirgin kamfanin Iraki Airways sun ketara rijiya da baibai bayan da a kan hanyarsu ta zuwa birnin Bagadaza bayan tasowa daga birnin Machhad na Iran, fada ya kaure a sararin samaniya tsakanin direban jirgin da mataimakinsa kan batun abinci. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito mataimakin matukin jirgin a wata wasikar bayar da bahasi da ya aika wa shugabannin kamfanin, na cewa fada ya barke tsakanin shi da abokin aikin nasa ne bayan da ya nemi ya hana wata ma'aikacciyar jirgin ta kawo masa abinci a bisa hujjar cewa bai nemi izini daga gare shi ba. 

Matukan biyu dai sun yi nasarar da kyar da haka sauka da jirgi a filin jiragen sama na birnin Bagadaza. Sai dai saukarsu ke da wuya suka koma bai wa hammata iska da zage-zagen juna inda sai da ta kai ga jami'an tsaro sun zo su shiga tsakaninsu.Mahukuntan aksar ta Iraki dai ba su bayyana ranar da lamarin ya faru ba, amma tuni ofishin ministan sufuri na kasar ta Iraki ya sanar da soma bincike kan matukan jirgin biyu da suka kai ga bai wa hamata iska a sararin subhana.