Iraki ta nemi goyon bayan Rasha a yaki da IS
May 21, 2015Talla
Firaministan na Iraki ya yi wadannan kalammai ne yayin tattaunawarsa da takwaransa na Rasha Dimitri Medvedev, inda ya ce ayyukan 'yan ta'addan na kara karfi tare kuma da daukar wani sabon salo.
Al-Abadi ya sanar da mahimmancin huldar kasarsa da Rasha a wannan lokaci, inda ya ce kuma wannan ziyara tashi ta tattabar da haka. Daga nashi bangare takwaransa na Rasha Dimitri Medvedev, ya yaba wannan ziyara, wadda ita ce ta farko tun lokaci da ya hau kan wannan mukami. Daga bisani Firaministan na Iraki zai gana da Shugaban Rasha Vladimir Putine.