1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta nemi tallafin Kungiyar NATO

Yusuf BalaDecember 4, 2014

Kasar Iraki dai ta kasance kasa daya tilo da ta shiga yaki da mayakan IS a Gabas ta Tsakiya ba kakkautawa. Lamarin da ya sanya take neman tallafin inganta sojanta.

Brüssel NATO Hauptquartier Anti IS Allianz 3.12.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/Olivier Hoslet

Gwamnatin Iraki na bukatar kungiyar tsaro ta NATO ta tallafa mata a wajen inganta harkokin sojanta a hukumance.

Amirka dai tuni ta shiga aikin ba da horo ga dubban mayakan kasar mafi akasari a yammacin lardin Anbar.

A yayin da ya halarci taron birnin Brüssel a ranar Laraba Firaminista Haider al-Abadi ya ce kasar Iraki ta kasance kasa daya tilo da ta shiga yaki da mayakan IS a yankin Gabas ta Tsakiya ba kakkautawa.

Wakilin DW a yayin taron na Brüssel Max Hoffmann ya ce akwai ci gaban ingantar dangantaka tsakanin mahukuntan na Iraki da kasashen yamma.

Ya ce wani abin da ke zama nasara a yayin wannan taro na zama yadda sabon Firaministan kasar ta Iraki da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry suka tabbatar da cewa lamura na ci gaba da sauyawa tsakanin kasashen kuma akwai ci gaba da ake samu bayan da sabuwar gwamnatin ke tafiya da kowane bangaren addini a gwamnatin kasar ta Iraki.