1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rataye mutane uku a Iraki

Abdul-raheem Hassan
December 14, 2021

Kotu ta rataye mutane uku har lahira bayan samun su da laifukan ta’addanci a wani gidan yari da ke birnin Nasiriya da ke yankin ‘yan Shi’a a kudancin kasar.

Symbolbild Iran Hinrichtung
Hoto: Loredana Sangiuliano/SOPA Images via ZUMA Press Wire/picture alliance

Daya daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisan, an same shi da hannu a harin bam da aka kai a garin Nasiriyya a shekarar 2013. Kotun ta kuma yanke wa mutum na biyu hukuncin daurin rai da rai saboda wani hari da aka kai a lardin Karbala da ke arewacin kasar.

Kasar Iraki ta zartar da hukuncin kisa kan sama da mutane 50 a shekarar 2020, adadi na hudu mafi girma a duniya, a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International.

Yawancin wadanda aka yankewa hukuncin kisan na da alaka da kungiyar IS, kungiyar da ta mamaye yankuna da dama na arewaci da yammacin kasar Iraki a wani hari da aka kai a shekara ta 2014 kafin dakarun gwamnatin su karya lagon kungiyar a 2017.