1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da Amurka sun fara ganawar kauce wa yaki

Zainab Mohammed Abubakar
February 26, 2026

Iran da Amurka sun fara tattaunawa a Switzerland, a wani yunkuri na karshe na hana yaki bayan Amurka ta jibge sojojin Amurka mafi girma cikin shekaru a Gabas ta Tsakiya.

Schweiz Genf 2026 | US-Sondergesandter Steve Witkoff und Jared Kushner bei indirekten Iran-Gesprächen
Hoto: Omani Foreign Ministry/AFP

Tattaunawar da Oman ke shiga tsakani ta biyo bayan barazanar da Donald Trump ya yi ta yi na kai hari kan Iran, inda shugaban Amurka a ranar Alhamis da ta gabata ya bai wa Tehran kwanaki 15 don cimma yarjejeniya.

Tawagar Amurka da ta Iran sun isa wurin tattaunawar da ke gidan jakadan Oman a Geneva cikin tsauraran matakan tsaro, bayan zanga-zangar da 'yan gudun hijira na Iran suka yi lokacin tattaunawarsu a makon da ya gabata.

Ministan harkokin wajen Oman Badr Albusaidi ya tabbatar da cewa an fara tattaunawa, yana mai cewa bangarorin biyu sun bayyana budaddiyar fahimta ga sabbin dabaru da laluben mafita daga wannan rikici.

Gabanin tattaunawar da shugaban Iran ya dage cewa jamhuriyar Musulunci ko kadan ba ta kera ko neman makamin nukiliya.