Yarjejeniyar Iran da hukumar IAEA
August 27, 2020Iran din ce dai da kanta ta gayyaci jami'an hukumar ta IAEA, wadanda suka yi ganawar kwanaki biyu da mahukunta a birnin Tehran, kafin su cimma wannan matsaya. Shugaban Hukumar Kula da Makashin Nukiliya na kasar ta Iran Dakta Ali Akbar Salehi ya yi karin haske: "Mun cimma matsaya cewa hukumar ta IAEA za ta gudanar da binciki abin da take tababa a kansa ne kawai a wadanan cibiyoyin biyu. Ta kuma amince ba za ta gabatar bincika abubuwan da ba ta da tababa a kansu ba. Babu wani abun da muke boyewa, amma 'yancin kasarmu zai sa mu ringa taka-tsan-tsan."
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya zargi Isra'ila da bai wa hukumar ta IAEA bayanan sirri na karya domin yi wa kasarsa batanci da hanata bunkasa makamashin nukiliyarta da take amfani da shi kan bukatun fararen hula.
To sai dai shugaban Hukumar kula da Makashin Nukiliyar ta Duniya Rafael Grossi ya nunar da cewa, binciken nasa ba shi da alaka da yarfen da kasashen na Iran da Isra'ila ke yi wa juna: "Wannan aiki ne na tsawon lokaci da muka jima muna yi a kasar, ba tare da yin la'akari da cece-kucen siyasar da ake ba. Muna gudanar da aikin ba tare da yin wata rufa-rufa ko nuna son kai ba, kuma haka zamu ci gaba da yi a yanzu dama nan gaba."
Amirka dai a ta bakin ministan harkokin wajenta Mike Pompeo ta siffanta wannan matsayar da aka cimma da tsantsar yaudara da ta ce za tai kokarin yi mata zagon kasa. A yayin da Rasha wacce ta bayyana farin cikinta matuka dangane da cimma matsayar ke cewa, hakan babban ci gaba ne da ke tabbatar da cewa za a iya warware matsaloli da dama ta hanyar tatatunawa ne kadai, ba ta hanyar yin barazana ko gwada kwanji ba.