1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da Isra'ila na ci gaba da kai wa juna farmaki

March 7, 2026

Iran da Isra'ila sun tabbatar da kai wa juna hare-hare yayin da aka shiga mako na biyu a rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Yadda hayaki ya turnuke a filin jirgin saman Mehrabad da ke Iran
Yadda hayaki ya turnuke a filin jirgin saman Mehrabad da ke IranHoto: Vahidonline/UGC

Isra'ila ta ce ta kaddamar da sabbin jerin hare-hare ta sama a Tehran, babban birnin Iran. An yi ta wallafa hotunan da ke nuna yadda wuta ke tashi tare da turnukewar hayaki daga filin jirgin sama na Mehrabad bayan harin, filin jirgin da ke zama babbar tashar zirga-zirga ta cikin gida a Iran. An kuma bayar da rahoton cewa an jiyo tashin ababen fashewa a birnin Kudus da kuma wasu biranen yankin Gulf ciki har da Dubai da kuma Manama.

Karin bayani: Na rufe kofar tattaunawa da Iran - Trump

Ita ma rundunar sojin Iran ta ce, sojojinta sun kaddamar da hare-haren jirage marasa matuka kan Isra'ila da ma wasu sansanonin Amurka da ke kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Kuwait. A cikin sanarwar da kamfanin dillancin labaran Iran din ya fitar, ya ce an kai hare-haren ne kan sansanin sojin Al Minhad da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, da kuma wani wuri da Iran din ta bayyana a matsayin mai matukar mahimmanci ga a Isra'ila.