1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IRAN DA MASAR ZASU GYARA DANGANTAKAR SU

January 6, 2004
Mahukuntan birnin Tehran a yau talata sun bayyana aniyar su ta gyara huldar dangantaka a tsakanin su da kasar Masar,bayan tsawon wani lokaci da kasashen biyu suka dauka basa ga maciji da juna. Dangantaka dai a tsakanin kasashen biyu ta fara tsami ne a tun lokacin da kasar Masar tasa hannun yarjejeniyar sulhun cimma zaman lafiya da kasar Bani israela,tare da bawa tsohon shugaban kasar Iran shah mafaka a cikin kasar tasu bayan hambarar da mulkin sa. A hannu daya haka suma mahukuntan kasar Iran,don suyi ramuwar gayya,sai suka sawa wani titi a cikin kasar su sunan,wanda yayi sular mutuwar shugaban kasar ta Masar wato Anwar sadat,wanda hakan ke nunin cewa shi gwarzo ne a idon mutanen kasar ta Iran. A cewar kakakin maikatar harkokin wajen kasar ta Iran;hamid reza asefi,wannan mataki da mahukuntan kasar suka dauka a dai dai wannan lokaci yazo ne bayan da yan majalisar birnin na Tehran suka kada kuriar neman canjawa titin da aka sawa sunan mutumin daya kashe maragayin shugaban kasar ta Masar wato Anwar Saddat,wanda hakan a can baya shiya haifar da kara dagula al,amurra a tsakanin juna. Kakakin yaci gaba da cewa a yanzu lokaci yayi da kasashen biyu zasu duba yiwuwar gyara dangantakar dake tsakanin su don yin hakan zai taimakawa Palasdinawa,musanmamma kungiyyar Jihadi Islami cimma burin su na zaman lafiya a tsakanin su da kasar Bani israela. Hamid Reza Asefi ya fadi wadan nan kalaman ne a lokacin taron yan majalisar dokokin birnin na Tehran,wanda a lokacin suka amince da sakewa titin na Khaled eslamboli izuwa dandalin itifada,don nuna girmamawa ga irin fadi tashin da Palasdinawa keyi na neman yancin kansu daga kasar Bani israela. Bugu da kari kakakin maikatar ta Iran ya yaba da bayanin da ministan harkokin wajen kasar ta Masar,Ahmed Meher yayi a ranar litinin din data gabata,inda yake cewa cimma yarjejeniyar sulhu a tsakanin su da kasar ta Israela a shekara ta 1978 a camp David abune daya wuce. Ahmed Maher yaci gaba da cewa a yanzu haka kasashen biyu sun dukufa kain da na,in wajen ganin sun dawo da dangantakar dake tsakanin su mai armashi irin tada,don samun ci gaba ta fannoni daban daban na rayuwar bil adama. Bisa kokarin gan cimma wannan buri na kasashe biyun,koda a watan daya gabata sai da Shugaba Khatami na Iran da Hosni Mubarak na masar suka gana,kuma a cewar kamfanin dillancin labaru na Tenran tattaunawar shuwagabannin biyu tayi armashi kwarai da gaske. A wata sabuwa kuma wata majiya mai karfi daga kasar ta iran ta nunar da cewa, Mubarak zaiyi tattaki izuwa kasar ta Iran a watan fabarairun wannan shekara da muke ciki don halartar taron kolin tattalin arziki na kasashe takwas masu tasowa da aka shirya yi a birnin na Tehran.