Harin Iran a Iraki ya haifar da fargaba
January 8, 2020Talla
Kamfanin jiragen sama na Lufthansa mallakar kasar Jamus da gungun jiragen Hadaddiyar Daular Larabawa, sun bi sahun kasashen da suka haramtawa jiragensu ratsawa ta kasashen Iran da Iraki saboda fargabar tsaro. Wannan dai ba shi ne karo na farko da jiragen sama suke gaggawar daukar matakan tsaron lafiya da dukiyoyin fasinjoji a lokutan rashin tabbas ba. A shekara ta 2014 ma jirage sun dauki irin wannan matakin gaggawar biyo bayan faduwar wani jirgin Malesiya mai dauke da fasinjoji 298.