Dubban Jamusawa sun makale a yankin Larabawa
March 2, 2026
Tun lokacin da yakin ya goce ranar Asabar da ta gabata bayan kasashen Amurka da Isra'ila sun kai hare-hare a kan Iran tare da kashe manyan jami'an gwamnatin kasar ciki har da jagoran addinni Ayatollah Ali Khamenei, lamura suka dagule a yankin Gabas ta Tsakiya a fannonin rayuwa da tattalin arziki.
Har zuwa wannan Litinin Iran na ci gaba da cilla makamai masu linzami a kan Isra'ila da kasashen Gabas da Tsakiya da suke da sansanonin sojan Amurka a cikin su.
Amurka ta ce bisa kuskure dakarun Kuwait da suka dauki matakin kakkabo makaman Iran da ake cilla kasar, sun harbo jiragen saman yaki uku na Amurka kuma duk matuka jiragen sun fita da rai. Sannan Iran ta yi barazana kan jiragen ruwan dakon kaya masu wucewa ta mashigin Hormuz.
Wannan mashigin ruwa ake wucewa da kimanin kaso 20 cikin 100 na manyan metur na duniya ya zama wayam, abin da ya shafi tattalin arzikin duniya.
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz na shirin ganawa da Shugaba Donald Trump na Amurka cikin wannan makon, yayin da yakin na Gabas ta Tsakiya ke kara dagulewa. Wannan bayan ziyarar da shugaban gwamnatin Merz zuwa China a makon jiya. Tuni dai Merz ya yi wani jirwaye mai kamar wanda wajen goyon bayan matakin hare-haren na Amurka:
"Gwamnatin Jamus ta amince da matsayin game da ci-gaban kasar Iran. Wannan bai bar wani gurbi ba game da matsayinmu kan sauya gwamnatin Iran. Gwamnatin da Mullah suke jagoranci sun kwashe shekaru suna ta'addanci da gallaza wa 'yan kasar Iran. Dubban mutane sun mutu sakamakon zanga-zanga a hannun gwamnatin a farkon wannan shekara. Gwamnatin na barazana da game da wanzuwar kasar Isra'ila. Su ne suke da alhakin ta'addancin Hamas da Hezbollah. A karshe matsayin Iran na kera makaman nukiya da makamai masu linzami na barazana ga kasashe makwabta da neman tarwatsa zaman lafiyar yankin. Gwamnatin tarayya domin haka, tana tare da 'yan Iran kan cewa gwamnatin tana matakin karshe."
Yayin da Amurka da Isra'ila suka ci gaba da kai hare-haren kan Iran. A daya bangaren Iran ta harba makami kan ofishin jakadancin Amurka da ke kasar Kuwait. Gwamnatin Lebanon ta yi tir da makin Hezbollah na harba makamai kan Isra'ila cikin dare.
Kana akwai 'yan kasashen ketere mazauna da kuma masu ziyara a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da suka makale sakamakon yakin da ke faruwa, inda tuni manyan kasashen duniya irin na Turai suka fara tunanin hanyoyin da za su taimaki 'yan kasashensu.
Jamus ta ce matafiya kimanin 30,000 da tafiyarsu ta shafi yankin Gabas ta Tsakiya wannan yaki ya shafa a cewar kamfanonin tafiye-tafiye na kasar. Mutanen 30,000 sun gaza zuwa wuraren da suka yi niyya na komawa gida daga hutu ko kuma akasin haka, sakamakon farmakin da kasashen Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan kasar Iran, da yadda yakin ke kara dagulewa.