1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Gangamin kona hijabi da bijire wa hukuma

Mahmud Yaya Azare
September 23, 2022

Jami'an tsaron Iran sun yi kashedin daukar tsattsauran mataki kan shirin masu fafutukar kare hakkin mata da wasu 'yan adawa na yin gangamin kona hijab a kasar.

Zanga zanga a Iran
Zanga zanga a IranHoto: Vahid Salemi/AP/picture alliance

Masu adawa da sanya hijabi a kasar ta Iran sun yi ta rera wakokin kin jinin gwamnati da maluman addini da ke da karfin tasiri a zanga zangar da suka yi wa take da "sai munga bayan sanya hijabi'.

'Yan mata da samari dai sun yi ta tirkar rawa a dandalin Kashanamah dake jihar Kurdustan suna jefa hijabansu cikin wutar da suka kunna a tskaiyar filin. Wata daga cikin 'yan zanga zangar ta yi tsokaci tana cewa

"Na rasa abin da zance saboda kaduwa da kisan da aka yi wa matashiya Amini don ta ki sanya hijabi. Daga yau na yi bankwana da sanya shi. Na kone guda a yau, idan na je gida zan tattara sauranma na kone su. Duk da cewa na san iyayena ba za su ji dadin hakan ba

Zanga zangar kona hijabi a IranHoto: SalamiPix/abaca/picture alliance

Zanga-zangar ta fantsama zuwa kusan dukkanin sassan Iran, Ita dai Mahsa Amini wacce 'yan sanda suka kamata a lardin Kurdistan bisa laifin kin sanya hijabi ta mutu lne yayin da take tsare a hannun jami’an tsaro, lamarin dai ya sanya zargin ko jami’an ne suka kashe ta duk da cewa a hukumance 'yan sanda sun ce matashiya ta mutu ne sakamakon bugun zuciya.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Iran ta ce al’ummar kasar sun fito tituna ne don kwatar hakkinsu da ake take musu inda shugaban kungiyar Ridha Hashimy ke cewa zuwa yanzu zanga-zangar na kankama a biranen kasar 30 sai dai akwai fargabar yiwuwar jami’an tsaro su yi amfani da karfin da ya wuce kima don dakile ta.

A cewar kungiyar alkaluman wadanda suka mutu a zanga-zangar ya haura mutum 30 ciki har da jami'in tsaro daya da wasu mutune 11 da aka kashe a garin Amol a ranar Larabar da ta gabata, da kuma wasu mutum shidda a Babol.

Masu zanga zanga kan mutuwar Mahsa AminiHoto: NNSRoj

Tuni dai kasashen Duniya suka yi Allah wadai da kisan Mahsa baya ga tilastawa mata sanya Hijabi da 'yan Hizba ke yi a kasar, yayin da a bangare guda Amurka ta sanar da sanya takunkumi kan jami’an ‘yan sandan Iran  bisa tilasta bin dokokin addinin musulunci da karfi da suke yi.

 Dama dai Rundunar juyin juya halin kasar ta yi kira ga ma'aikatar shari'a a kan ta hukunta duk masu yaɗa jita-jitar karya, tana mai kira ga mahukunta da su rufe intanet a kasar.

A daura da haka ,Fitacciyar 'yar jaridar nan ta CNN Christiane Amanpour ta soke wata hira da ta shirya yi da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, bayan da aka bukaci cewa sai ta daura dankwali kafin hirar da aka shirya yi a birnin New York na kasar Amurka.

 Amanpour ta ce babu ko daya daga cikin tsoffin shugabannin Iran da ya taba bukatar ta yi hakan a duka hirarrakin da ta yi da su a wajen kasar.

Ta kara da cewa wani hadimin shugaban kasar ya sanar da ita cewa an bukaci ta yi hakan ne sakamakon 'halin da kasar ke ciki a yanzu.