1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure Fariba Adelkhah tsawon shekaru biyar a Iran

Abdoulaye Mamane Amadou
May 16, 2020

Faransa ta yi Allah wadarai da hukuncin zaman gidan wakafi na shekaru biyar da wata kotun birnin Theran ta yankewa 'yar asalin kasartan nan Fariba Adelkhah a yau din nan.

Fariba Adelkhah - Iran verurteilt französische Akademikerin zu Gefängnis
Hoto: AFP/Sciences Po/T. Arrive

A cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a yau, ma'aikatar ta ce hukuncin da aka yankewa malamar jami'ar ko kadan baya da tushe da wasu kwakwaran hujjoji da ka iya tabbatar da zargin cin amanar kasa da hukumomin na Iran ke tuhumar Fariba Adelkhah din aikatawa, sannan kuma kasar ta ce za ta ci gaba da dagewa, face sai ta ga mahukuntan na Iran sako ta.

A ranar biyar ga watan Yulin bara ne dai gwamnatin Faransa ta tabbatar da kamun Adelkhah, tare da shigar da jerin wasu muhumman bukatu na ganin an sako ta tun a gabanin a gurfanar da ita a gaban shari'a.