1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kama wasu 'yan kasashen waje 9 a zanga-zangar Iran

Binta Aliyu Zurmi
September 30, 2022

A ci gaba da zanga-zangar da mata a Iran ke yi bisa mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami'an hisba a lokacin da suke tuhumarta a kan zargin yawo kai ba kallabi.

Unterstützerkundgebung von Demonstranten gegen Mehsa Amini Tod vor dem Brandenburger Tor in Berlin
Hoto: Ali Eshtyagh/DW

Mahukuntan Tehran sun sanar da kame wasu mutane 9 da suka ce 'yan kasashen ketare ne kuma suna daga cikin masu rura wutar rikicin da ya biyo bayan boren da matan suka fara.

Duk da ma'aikatar leken asirin kasar ba ta fidda sunayen mutanen da ta ce ta kama ba, amma dai ta ce sun fito ne daga kasashen Jamus da Poland da Italiya da Faransa da Holland gami da Sweden.

Ko a jiya Alhamis wasu masu zanga-zanga a Oslo na kasar Norway, sun yi yunkurin kutsa kai cikin ofishin jakadnacin Iran da ke birnin kafin jami'an tsaro su hanasu. 

Suna masu son jan hankalin gwamnatin Tehran, kan zanga-zangar da ke gudana a fadin Iran a game da mutuwar matashiyar Mahsa Amin a hannun jami'an Hisba.