Ko Iran za ta mallaki makamin nukiliya?
June 20, 2025
Gabannin Sallar Jumma'a an kada kararrawa a yakuna da dama na Israila, domnin ankarar da mutane cewa Iran na dab da harba makami mai linzami da nufin ganin mutane sun tsere zuwa ga maboya. Haka dai rayuwa take a Isra'ila da ma Iran a yanzu, a Haifa birni mai tashar jiragen ruwa da ke a arewacin Isra'ila masu aikin ceto sun tabbatar da fadawar makmai masu linzami a kan gine-gine da dama wadanda suka ruguje. Majiyoyin soja sun ce, Iran ta harba makamai masu linzami kusan 20 zuwa Isra'ila.
Karin Bayani: Rasha da China na neman a warware rikicin tsakanin Isra'ila da Iran
Wani babban hafsan sojan Isra'ila Laftanar Janar Eyal Zamir cikin wani sakon bidiyo ya yi kira ga al'ummar kasar da su shirya wa kwanaki masu wahala a gaba, game da irin shirin da Isra'ilan take yi na kara kaimi a kan Iran. Ya ce za su kaddamar da yaki mafi sarkakiya a tarihinsu, dole ne mutane su kasance cikin shiri. Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira ga bangarorin biyu da su samar da zaman lafiya, to amma jakadan Isra'ila a majalisar Dany Danon ya ce makaman Iran za su iya cimma duniya.
Tun bayan harin da aka kai wa Iran a ranar 13 ga wannan wata na Yuni da muke ciki, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi ta kokarin shawo kan shugaban Amurka Donald Trump da nufin Amurka ta shiga fadan wanda bisa ga dukkasn alamu a yanzu Isra'ila abin ya zame mata ba-zata na irin karfin da ta rasa a Iran. Daura da halin da ake ciki wakilan Jamus da Faransa da Birtaniya, na tattaunawa da wakilan Iran a Vienna.
Karin Bayani: Jamus: Ina makomar hulda ta Gabas ta Tsakiya?
A cikin batutuwan da za su tabo, har da rage inganta makashin nukiliyarta ta hanyar watsi da shirinta na kera makamai masu linzami. Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiliya na Duniya Rafael Grossi ya ce, tashar makamashin nukiliyar Iran ta Bushehr ita ce tashar nukiliya a Iran da sakamakon harin zai iya zama mafi tsanani. Ita ce tashar makamashin nukiliya mai aiki, kuma tana karbar dubban kilogiram na makaman nukiliya. Kasar Iran wacce ta mayar da martani da makami mai linzami da jiragen yaki mara matuki a Isra'ila, ta musanta cewa tana son kera makaman kare dangi amma tana kare hakkinta na raya shirin nukiliyar farar hula.