1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barasa ta halaka mutane a Iran

Abdul-raheem Hassan
May 3, 2022

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Iran sun tabbatar da mutuwar mutane takwas, bayan shan barasa mai guba a lardin Hormozgan da ke kudancin kasar, wasu mutane 30 na gadon asibiti 17 daga cikinsu a mawuyacin hali.

Symbolbild Alkohol
Hoto: David Jones/PA Wire/empics/picture alliance

'Yan sandan kasar ta Iran dai, sun kama fiye da litar barasar gargajiya fiye da 1,000 tare da kame mutane takwas da ake zargi da sarrafa giyar ta haramtaciyyar hanya. Gwamnatin Iran ta haramta sha da sayar da barasa, amma duk da haka ana samun yawaitar mutuwar mutane da dama da ke da nasaba da kwankwadar barasar gargajiya da ake zargi tana hade da guba. Koda a watan Maris na shekarar 2020, fiye da mutane 44 ne suka mutu sakamakon shan burkutu da nufin magance cutar annobar corona.