Kasar Iran na bin sharuddan da aka gindaya mata
May 27, 2016![Darakta janar na hukumar IAEA Yukiya Amano](https://static.dw.com/image/18984817_800.webp)
Wadannan sharudda dai an gindaya wa Iran su ne yayin cimma yarjejeniyar da suka yi da kasashe shida da ke fada a ji a duniya kan makamashin nukiliyar Iran din. A wani rahoto da hukumar ta IAEA ta fitar, ta nunar da cewa Iran na cika dukkan alkawuran da ta dauka yayin cimma wannan yarjejeniya a bara, kana tana barin wakilan hukumar su kai ziyarar gani da ido a tashoshin nukiliyarta. Wannan rahoto dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka da Japan suka yi kira da a kawo karshen yaduwar makaman nukiliya a duniya, yayin wata ziyara da shugaban Amirkan Barack Obama ya kai yankin Hiroshima na Japan din da harin makaman nukiliyar Amirka ya dai-daita a shekara ta 1945. Iran dai ta cimma yarjejeniyar rage sarrafa makamashin nukiliyarta da kasashe shida masu fada a ji a duniya, ta yadda su kuma a hannu guda za su cire mata takunkuman karya tattalin arzikin da suka kakaba mata na tsahon shekaru.