Iran na kokarin sasanta Indiya da Pakistan
May 5, 2025
Talla
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi ya gana da manyan jami'an gwamnatin Pakistan a wannan Litinin, ganawar kuma da ke da nufin shiga tsakani domin warware rigimar da ta taso tsakanin Pakistan da Indiya.
Dagantaka dai ta kara yin tsami a tsakanin Pakistan din da Indiya ne, bayan wani kazamin hari da aka kai kan wasu Indiyawa 'yan yawon shakatawa a yankin Kashmir.
Ziyarar ta Abbas Araghchi a Islamabad ita ce ta farko da wani babban jami'i ke kaiwa da nufin duba rigimar da ta janyo asarar rayukan mutane 26 a ranar 22 ga watan jiya a garin Pahalgam na Kashimr.
Pakistan dai ta yi ta musanta laifin da Indiya ta dora mata na kasancewa da hannun a mutuwar bakin 'yan yawon shakatawa.