Iran ta kudiri keta yarjejeniyar nukiliya
June 17, 2019Talla
Iran ta ce nan da kwanaki goma masu zuwa za ta habaka makamashinta na Uranium domin zarta iyakancewar da hukumar makamashin nukiliya ta kasar ta cimma da manyan kasashen duniya.
Mai magana da yawun hukumar makamashin nukiliya ta kasar Behrouz Kamalvandi wanda ya sanar da hakan ya kuma yi kashedin cewa kasar na bukatar habaka makamashin na Uranium da kimanin kashi 20 cikin dari matakin da zai kaita dab da kera makamin nukiliya.
Kamalvandi yace kasashen Turai na da takaitaccen lokaci su hanzarta ceto yarjejeniyar nukiliyar, idan ba haka ba kuwa za ta bunkasa makamashin fiye da matsayin da aka cimma a yarjejeniya da ita da manyan kasashen duniya kan shirinta na nukiliya.