1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran na son kaucewa shiga yaki da Amurka

February 1, 2026

Yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da yin barazanar kai wa Iran hari, Teheran ta ce tana son bai wa diflomasiyya fifiko.

Shugaban Kasar Iran Masoud Pezeshkian
Shugaban Kasar Iran Masoud PezeshkianHoto: Iranian Presidency/Anadolu/picture alliance

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa yaki ba abu ne da zai yi wa kasarsa da Amurka dadi ba, tare da cewa yana son bai wa diflomasiyya fifiko domin warware takammar da ta kunnokai a tsakanin Teheran da Washington.

Wadannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da yin barazanar kai wa Iran hari, a wani lamari da duniya ke ganin na iya zama hadari da ka iya haifar da gagarumin rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Qatar ta yi gargadi kan sakamakon rikicin Amurka da Iran 

Firaministan Qatar Cheikh Mohammed bin Abulrahaman Al Thani ya ziyarci Iran a jiya Asabar inda ya jaddada wa Teheran cewa kasarsa na goyon bayan duk wani kokari na kaucewa tashin hankali domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron a yankin.

Turkiyya na kokarin kaucewa rikici tsakanin Iran da Amurka

A daidai wannan lokaci rundunar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya Centcon ta yi gargadi tare da yin kwakkwaran kashedi kan wani shiri na atisayen sojin ruwa na kwani biyu da ta ce dakarun juyin juya halin Musulumcin Iran na shirin gudanarwa a 'yan kwanankin masu zuwa.