1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na zaben shugaban kasa

June 28, 2024

Al'umma a Iran na zaben sabon shugaba da zai maye gurbin marigayi tsohon shugaban kasar, Ebrahim Raisi da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar angulu.

Dan takarar Mohammad Bagher Ghalibaf a lokacin da yake kada kuri'a
Dan takarar Mohammad Bagher Ghalibaf a lokacin da yake kada kuri'aHoto: Majid Asgaripour/WANA/REUTERS

Ana sa ran 'yan kasar miliyan 61 ne za su kada kuri'ar zaben sabon jagora bayan mutuwar Ebrahim Raisi a watan Mayun 2024, duk da cewa jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei shi ne mai cikakken fada a ji a Iran kana babban kwamandan rundunar sojin kasar.

Karin bayani: Mohammad Mokhber ne shugaban kasa na riko a Iran

'Yan takara hudu ne za su fafata a zaben, sai dai wadanda ake ganin za su iya lashe zaben su ne Saeed Jalili, tsohon mai shiga tsakani a tattaunawar kasa da kasa a kan nukiliya da kuma Mohammad Bagher Ghalibaf, tsohon ministan kiwon lafiyan kasar.

Idan har babu dan takarar da ya samu rinjaye, za a sake komawa zagaye na biyu na zaben a ranar biyar ga watan Yuli.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW