1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na zaman makokin Shugaba Ra'isi

Abdullahi Tanko Bala
May 21, 2024

Dubban jama'a sun yi tattaki kan titunan birnin Tabriz a arewa maso yammacin Iran domin nuna alhini da rasuwar shugaban kasar Ebrahim Ra'isi

Iran Tabriz Beisetzung Präsident Raisi
Hoto: IRAN PRESS/AFP

Shugaban na Iran Ebrahim Ra'isi ya rasu ne a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu tare da 'yan tawagarsa su bakwai ciki har da ministan harkokin waje Hossein Amir-Abdollahian.

Karin Bayani: Mohammad Mokhber ne shugaban kasa na riko a Iran

Jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei wanda ke da karfin tasiri a Iran ya ayyana zaman makoki na kwanaki biyar a fadin kasar domin jimamin rasuwar shugaban kasar.

Karin Bayani: Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya rasu

Khamenei ya kuma nada mataimakin shugaban kasar Mohammed Mokhber mai shekaru 68 da haihuwa ya ja ragamar shugabancin kasar gabanin zaben cike gurbi wanda za a yi a ranar 28 ga watan Yuni.