1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Raisi na ziyara a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 12, 2023

Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya fara wata ziyarar aiki a kasashen Afirka a karo na farko tun bayan zabarsa a matsayin shugaban kasa.

Iran | Ebrahim Raisi | Kenya | Ziyara | Afirka
Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya isa KenyaHoto: Khalil Senosi/AP/picture alliance

Shugaba Ebrahim Raisi na Iran din dai, ya ziyarci Kenya kana kuma zai karasa Yuganda da Zimbabwe. Yayin da yake ganawa da Shugaba William Ruto na Kenyan dai, sun amince da sanya hannu kan yarjejeniya har guda biyar. Tehran na fatan samun wasu abokan huldar na dabam domin kara bunkasa tattalin arzikinta, biyo bayan tarin takunkuman tattalin arziki da take ci gaba da fuskanta daga al'ummomin kasa da kasa.