Shugaba Rohani na Iran ya yi kakkausar suka ga Amirka
September 22, 2019Talla
A yayin da yake jawabi a wani bukin faretin soja a birnin Téhéran, Shugaba Rohani ya ce yankin na tekun fasha na cikin wani yanayi mai cike da tarihi, kan daga bisani ya soki duk wani batun jibge bataliyoyin soja daga wasu kasashen ketare a yankin, yana mai cewa hakan ka iya kara dagula al'amurran tsaro da zaman lafiyar yankin.
Jawabin shugaban na zuwa ne kwanaki bayan matakin da kasar Amirka ta dauka na kara jibge adadin sojojinta yankin tekun fasha a wani mataki na tauna tsakuwa kan kasar Iran, wacce Amirka da Saudiyya ke zarginta da alhakin kai hari a wasu matatun man fetir din kasar Saudiyya a makon jiya.