1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Mahsa Amini ta shekara guda da mutuwa

September 15, 2023

Mutuwar matashiya 'yar kasar Iran Mahsa Amini a hannun 'yan sanda a bara, ta janyo zanga zangar adawa da gwamnatin Tehran a kasar baki daya.

Iran | Jina Mahsa Amini | Mutuwa | Shekara Guda
Matashiya 'yar Iran da ta mutu a hannun 'yan sandan kasar Jina Mahsa AminiHoto: UGC

Gabanin cika  shekara guda da mutuwar Jina Mahsa Amini a ranar 16 ga watan Satumba, iyalanta sun wallafa  sako a shafin Instagram da ke cewa suna so za su yi zaman nuna alhini a inda kabarinta yake. Sanarwar ta kara da cewa danginta kamar ko wadanne irin iyalai, suna so za su yi addu'oi da sauran abubuwan da addini ya amince da su da ake yiwa mamaci. Sai dai kuma, a bara hukumomin Iran sun sa ido sosai akan iyalan Amini. A 'yan kwanakin nan rahotanni sun nunar da cewa, an jibge jami'an tsaro a kusa da gidan iyayen marigayiyar a birnin Saqqez. Hukumomin na Iran ba suna sa ido kan iyalan Amini ne kadai ba, suna kuma sa ido a kan makabartu da dama da aka binne mutanen da aka kashe a wuraren zanga-zanga.

Karin Bayani: Turai na goyon bayan zanga-zangar Iran

Hukumomin dai, na son hana tarukan ne da hujjar cewa za a iya samun barkewar zanga-zanga. Duk da mummunar dirar mikiya a kan masu zanga zangar, shekara guda bayan nan, matan Iran sun ci gaba da jajircewa. Yana da wahala a iya samun cikakkun alkaluma, sai dai a cewar kungiyoyin kare hakkin dan Adam masu zaman kansu na cewa 'yan sandan Iran sun halaka masu zanga-zanga kimanin 527 ciki har da kananan yara 17 a yayin zanga-zangar da ta gudana tsakanin 16 ga watan Satumbar 2022 zuwa karshen watan Janairun 2023. Iyalan mutanen da aka kashe a yayin zanga-zangar, suna cikin tsananin damuwa. Kawo yanzu an kama fiye da mutane 40 iyalan wadanda  aka kashe a zanga-zangar, kuma a kullum kamen karuwa yake.

Zanga-zanga ta barke a Iran, jim kadan bayan sandar da mutuwar Jina Mahsa AminiHoto: dpa/AP/picture alliance

Suma masu fafutuka da masu rajin kare hakkin al'umma da dama, ko dai ana tsare da su ko ana tuhumarsu ko kuma ana yi musu barazana da rayuwarsu. Watakila wannan wata dabara ce, ta hana ci gaba da zanga-zangar. An kama Jina Mahsa Amini ne a shekarar da ta gabata lokacin da ta kai ziyara Tehran babban birnin kasar Iran, inda 'yan sanda suka tafi da ita saboda kanta babu dankwalli ba ta yi shiga ta Musulumci ba. A Iran dai an tsaurara bukatar mata su daura dankwali, idan za su fita a bainar jama'a. 'Yan sa'o'i kadan bayan nan aka garzaya da Amini zuwa asibiti daga ofishin 'yan sanda, kafin bayan kwanaki uku kuma a ranar 16 ga watan Satumba a bayar da sanarwa a hukumance cewa ta rasu.

Karin Bayani: Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku

Zanga-zanga ta barke bayan jana'izar Amini a mahaifarta Saqqez da ke yankin Kurdawa a yammacin Iran, kuma nan da nan ta yadu a fadin kasar. Mutuwar Mahsa Amini ta girgiza mutane ba ma a Iran ba, har da kasashen waje. A watan Oktobar 2022 ga misali, 'yan Iran da ke gudun hijira a Jamus sun gudanar da taron gangami a Berlin. An kiyasta cewa mutane kimanin dubu 800 ne, suka halarci taron gangamin. Sai dai kuma a cikin gida kafa kungiyar adawa a Iran yana da wahala matuka, saboda dirar mikiya da jami'an tsaro ke yi a cewar Arash Azizi kwararre kan yankin Gabas ta Tsakiya da ke Jami'ar New York.