1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Iran ta ba wa mata izinin tuka ababen hawa masu taya biyu

Mouhamadou Awal Balarabe
February 4, 2026

Mataimakin shugaban kasa na farko Mohammad Reza Aref, ya sanya hannu kan wani kuduri da majalisar ministoci ta amince da shi a Janairu, da nufin kawo karshen shekaru na rashin tabbas kan dokar tukin babura ga mata.

Matan Iran sun fara samon horo a fannin tukin babura
Matan Iran sun fara samon horo a fannin tukin baburaHoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto/picture alliance

Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bai wa mata izini a hukumance na iya samun lasisin tuki na ababen hawa masu taya biyu wato kekuna da babura. Mataimakin shugaban kasa na farko Mohammad Reza Aref ne ya sanya hannu kan wani kuduri da majalisar ministoci ta amince da shi a karshen Janairu, da nufin fayyace ko kawo karshen shekaru da dama na rashin tabbas kan dokar tukin babura ga mata.

Wannan mataki ya bukaci 'yan sanda da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a Iran da su "ba da horo ga mata da ke son tuka babaru, tare da shirya jarrabawa domin tantance wadanda suka cancaci samun lasisi". Wannan sanarwar ta zo ne bayan zanga-zanga kan tsadar rayuwa, wacce ta haddasa mutuwar dubban mutane.

Tun bayan juyin juya halin Musulunci na 1979 ne, Iran ta haramta wa mata wasu ayyuka, amma a baya- bayan nan, mata na nuna adawa da wadannan ka'idodi. Wannan ya karu a 2022 bayan mutuwar Mahsa Amini, wata matashiya 'yar Iran da aka kama saboda zargin karya dokar sutura.