Iran ta baiwa Hugo Chavez lambar girmamawa
July 31, 2006Iran ta karrama shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez da lambar yabo mafi daraja saboda goyon baya da yake nunawa Tehran a taƙaddamar ta ta nukiliya. Shugaban na Venezuela Hugo Chavez ya buƙaci ƙasashen duniya su tashi tsaye a kan Amurka. Chavez ya baiyana shugaban Amurka George W Bush da cewa shaidani ne, ya kuma yi tur da Allah wadai da Israila a bisa abin da ya baiyana da cewa taáddanci da kuma rashin hankali a hare haren da take yi a Lebanon. Hugo Chavez ya yi kira ga alúmar duniya, su haɗa karfi wuri guda domin ganin bayan Amurka. Shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya miƙawa Hugo Chavez tambarin zinare a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a jamiár Tehran tare kuma da yi masa jinjina a dangane da goyon bayan da yake baiwa Iran. A watan fabrairun da ya gabata, ƙasar Venezuela ta ƙi amincewa da shawarar hukumar makamashin nukiliya IAEA na gabatar da Iran ga kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya.