1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Iran ta zargi Amirka da barazana

Zulaiha Abubakar
September 22, 2018

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya jaddada cewar kasar ba za ta yi watsi da kayan yaki ba wadanda suka hada da makamanta masu linzami da ke firgita kasar Amirka, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Tun da fari ministan harkokin kasashen wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewar shugaban kasar Amirka Donald Trump ya zamarwa yankin gabas ta tsakiya barazana,a watan daya gabata ne dai Amirka ta kakabawa Iran takunkumin da ya fara yin tasiri a fagen tattalin kasar biyo bayan janyewar Amirka daga batun makaman kasar ta Iran.