1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta gargadi Birtaniya kan jirgin ruwanta

Abdullahi Tanko Bala
July 5, 2019

A wata takaddama da ke neman kunno kai Iran ta gargadi Birtaniya ta sako jirgin ruwanta da ta kama ko kuma ita ma ta dauki matakin ramuwar gayya.

Öltanker auf dem Weg nach Syrien in Gibraltar festgesetzt
Hoto: Reuters/Stringer

Iran ta bukaci gwamnatin Birtaniya ta gaggauta sako mata jirgin ruwanta na dakon mai da ta kame a Gibraltar inda ta zargi Birtaniyar da zama 'yar kanzagin Amirka.

Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Iran din ya baiyana matakin Birtaniya da cewa ba za a amince da shi ba a yayin wata ganawa da jakadan Birtaniya a Iran Rob Macaire wanda hukumomin Iran din suka aikawa sammaci domin gabatar da kokensu.

Sakataren majalisar gudanawa ta Iran wadda ke bada shawara da sasantawa kan takaddama ya gargadi Birtaniya da cewa idan har ta ki sako jirgin ruwan, to babu makawa itama za ta dauki matakin ramuwar gayya akan jiragen ruwan Birtaniya.