Iran ta ce tattaunawar nukiliyarta da Amurka ba ta da amfani
June 14, 2025
Iran ta zargi Amurka da goyon bayan harin da Isra'ila ta kai mata, sannan kuma ta ce tattaunawar yarjejeniyar dakatar da kera makamin kare dangi na nukiliya da take yi da Amurkar ba ta da wani amfani.
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta bakin mai magana da yawunta Esmaeil Baghaei, ta ce Amurka ta nuna fuska biyu, inda a gefe guda take tattaunawar cimma masalahar jingine kera nukiliya da Iran, amma a daya gefen kuma ta goyi bayan harin da Isra'ila ta kai mata.
Ranar Lahadi ya kamata a gudanar da ganawa ta shida tsakanin wakilan Amurka da na Iran a birnin Musqat na Oman, to sai dai babu tabbacin yiwuwar zaman sakamakon barkewar wannan rikici.
Da safiyar wannan Asabar Iran ta samu nasarar kakkabo makaman da Isra'ila ta kai mata hari da su.
Harin ramuwar gayya da Iran ta kai wa Isra'ila da safiyar wannan Asabar ya halaka mutane uku, tare da jikkata wasu da dama a biranen Jerusalem da Tel Aviv, inda hukumomin Isra'ila ke ci gaba da gargadin 'yan kasar su nemi mafaka.
Tun farko Isra'ila ce ta fara kai wa Iran hari kan cibiyoyin nukiliyarta tare da halaka manyan hafsoshin tsaronta, cikin daren Alhamis zuwa wayewar garin Juma'a, kuma ta ci gaba da kai farmaki da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, mafarin bude kofar wani sabon rikici a tsakanin kasashen biyu da suka jima suna adawa da juna tsawon shekaru.
Karin bayani:Harin ramuwar gayya ne mafita ga Iran?
A wani jawabi da jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya gabatarwa al'ummar kasar ranar Juma'a, ya ce ba za su saurara wa Isra'ila ba sakamakon munin abin da ta aikata musu.
Shi ko jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir-Saeid Iravani, ya ce mutane 78 ne suka rasa rayukansu zuwa yanzu, yayin da sama da 320 suka samu raunuka, tun bayan da Isra'ila ta fara kai musu harin.