1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila na son a karawa Iran takunkumi

Abdul-raheem Hassan MAB
December 10, 2021

Manyan kasashen duniya da Iran sun kasa cimma matsaya na farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015, bangaren Turai na son aiwatar da tattaunawar watanni biyar baya amma Tehran ta yi tsayin daka kan sharudan da ta gindaya.

Österreich | Atomgespräche mit dem Iran
Hoto: EU Delegation in Vienna/Handout/AFP

Kasar Isra'ila wacce dama ba ta cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran na 2015, amma yanzu ta samu damar shiga tattaunawar na ci gaba da yi wa Teheran barazanar sabbin takunkumin karya tattalin arziki muddin aka kasa shawo kanta ta a diflomasiyyance.

Karkashin yarjejeniyar asali wacce tsohon Shugaban Amirka Donald Trump yi watsi da ita 2018, Iran ta iyakance shirinta na nukiliya don samun sassauci daga takunkumin Amirka, Kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai kasashen yammacin duniya sun nuna fargabar Teheran za ta yi amfani da shirin wajen habaka makamai, zargin da Iran ta musanta.