1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta yi fatali da tattaunawa da Amurka

March 10, 2026

Iran ta kawar da maganar tattaunawa da Amurka domin kawo karshen yaki tare da yin alwashin cewa ta shirya wa yin yakin dogon lokaci.

Ministan harkokin wajen Iran yayin taron manema labarai
Ministan harkokin wajen Iran yayin taron manema labaraiHoto: Foad Ashtari/SOPA Images/ZUMA/picture alliance

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa a wannan Talata a shirye kasarsa ta ke ta fafata yaki na dagon lokaci da kawancen Amurka da Isra'ila, furucin da ya ci karo da na shugaban Amurka Donald Trump wanda a daren jiya ya ce yakin zai kawo karshe nan ba da jimawa ba.

Babban jami'in diflomasiyyan na Iran ya shaidawa gidan talabijin din Amurka PBS News cewa a shirye kasarsa take ta ci gaba da yin musayar makamai masu linzami da abokan fadanta, sannan ya kara da cewa ''batun tattaunawa da Amurka ba ya cikin ajandar Iran''.

Yaki tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila na kara kazancewa

A daidai wannan lokaci a safiyar yau Talata ma'aikatar tsaron Hadaddiyar Daular Laraba ta ce ta fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jirage maras daga Iran yayin da yakin ya cika kwanaki 11 da barkewa.

 

Mojtaba Khamenei ya samu karbuwa a Iran

Gangamin goyon bayan sabon jagoran addinin Iran a TeheranHoto: Vahid Salemi/AP Photo/picture alliance

Hakazalika a jiya Litinin dubun dubatar jama'a sun fito wani kasaitaccen taron gangami a birnin Teheran domin nuna goyon baya ga sabon jagoran addinin Iran Mosjitaba Khamnei wanda aka nada a matsayin magajin mahaifinsa da aka kashe a ranar farko ta yanki. 

Gangamin goyon bayan sabon jagoran addinin Iran a TeheranHoto: Majid Asgaripour/WANA (West Asia News Agency)/REUTERS