1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta dage akan matakin ta

September 22, 2006

Daya daga cikin manya manyan malamai a Iran , wato Akbar Hashemi Rafsanjani yace Iran ba zata dakatar da matakin ta na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium ba.

A cewar malamin, sharuddan da kasashe masu fada aji suka gindayawa kasar , don kawo karshen rikicin nukiliya, abubuwa ne da ba masu karbuwa ba.

Malamin wanda yake daya daga cikin masu bawa shugabann addini na kasar shawara, ya fadi hakan ne, a lokacin da yake jawabi ga masallata a masallacin jami´´ar Tehran a yau juma´ar nan.

Idan dai za´a iya tunawa , shugaba Bush na Amurka yace dakatar da sarrafa sadarin Uranium na daga cikin sharuddan komawa teburin sulhu da kasar ta Iran.

A cikin jawabin daya gabatar a gaban babban taron Mdd a jiya, shugaba Mahmud Ahmadinajad, yace kasar sa a shirye take ta warware rikicin nukiliyar ta, amma idan an sa adalci a ciki.