Iran ta bijire wa yarjejeniyar nukiliya
May 8, 2019Ministan harakokin wajen kasar ta Iran Mohammad Javad Zarif ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Laraba inda ya ce sun dauki wannan mataki ne a sakamakon ficewar da Amirka ta yi daga cikin yarjejeniyar nukiliyar da kuma jerin takunkuman tattalin arzikin da ta sake kargama wa kasar ta Iran.
Ministan harakokin wajen kasar ta Iran wanda ke wata ziyarar aiki a yanzu haka a kasar Rasha bai bayyana irin alkawurran da za su dakatar da mutuntawa ba, sai dai ya ce wasu matakai ne wadanda yarjejeniyar ta bai wa kowane bangare izinin kin mutuntawa idan har daya daga cikin bangarorin da ke da hannu a yarjejeniyar ya ki mutunta alkawarin da ya dauka. Amma dai ya ce Iran ba ta da niyyar ficewa kwata-kwata daga cikin yarjejejniyar.
Kasar ta Iran ta ce tuni ta sanar da wannan mataki nata ga jakadun kasashen Jamus da China da Faransa da Birtaniya da kuma Rasha wandada ke ci gaba da kasancewa a cikin yarjejejniyar bayan ficewar Amirka daga cikinta yau shekara daya.