1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta dau alwashin sake gina tashoshin nukiliyarta

November 2, 2025

Matakin na zuwa a daidai lokacin da kasashen yammacin duniya suka dawo da takunkuman da suka kakaba wa Teheran kan shirinnta na nukiliya.

Shugaban kasar Iran Massud Peseschkian
Shugaban kasar Iran Massud PeseschkianHoto: Iranian Presidency/Zuma/picture alliance

Shugaban Iran Massud Pezeshkian ya jaddada cewa kasarsa za ta sake gina tashoshin nukiliyarta da Amurka da Isra'ila suka kai wa hari a watan Yuni da ya gabata, a daidai lokacin da sarkin Oman mai shiga tsakanin Teheran da Washington ya bukaci bangarorin biyu su koma kan teburin tattaunawa.

Shugaban na Iran ya furta wadannan kalamai a wannan Lahadi a lokacin da ya kai ziyara a ofishin hukumar makamashin nukiliya ta kasar, inda ya ce rushe gine-ginen tashoshin ba zai sa kasar ta ja da baya ba, yana mai jaddada cewa za a sake gina tashoshin da karfin gaske.

Dama dai a karshen watan Oktoba da ya gabata, jagoran addinin Iran Ayatullah Ali Khamene ya bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump na mafarki idan har yana tunanin cewa ya lalata tashoshin nukiliyar kasar.