Iran ta fara sarrafa makamashin nukiliya
December 5, 2010Babban Jami'in da ke kula da makamashin nukiliyar Iran Ali Akbar Salehi ya ce masana kimiya sun gabatar da sarrafaffen makamashin uranium na farko wanda za'a yi amfani da shi a matsayin makamashi. Wannan sanarwar ta nuna cewa ƙasar Iran ta lashi takobin bunƙasa masana'antun ta da yin amfani da makamashin nukiliya.
Wannan dai na zuwa ne a jajibirin taron da ƙasar za ta gudanar da ƙasashen duniya masu manyan masana'antu a wani yunƙurin da ƙasashen ke yi wajen shawo kan Iran da ta daina inganta dabarun fasahar ta.
Amfani da makamashin nukiliyan dai yana zama barazana ga ƙasar Amurka da wasu abokan ɗasawar ta saboda ana iya amfani da makamashin wajen sarrafa makaman ƙare dangi.
Ko da yake, Iran ta haƙiƙance cewar zata yi amfani da makamashin ne wajen bunƙasar tattalin arzƙin ta da kuma samar da zaman lafiya, Kana Salehi ya bayyana cewa hukumar da ke kula da makamashin nukiliya a Majalsar Ɗinkin Duniya, zata sa ido wajen duk aikin makamashin nukiliyan da ƙasar zata aiwatar.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi