Iran ta fitar da sabon haramci ga wasu kasashe a Hormuz
March 27, 2026
Dakarun juyin juya hali na Iran sun sanar da haramta zirga-zirgar jiragen ruwa a tsakaninsu da tashoshin jiragen ruwa na kasashen da suke goyon bayan Amurka da Isra'ila.
Sanarwar da kafafen yada labarai ta gwamnatin Iran ta fitar ta ce an hana duk wani jirgi zirga-zirga zuwa ko kuma tasowa daga irin wadannan kasashe ta kowace hanya.
Haka kuma, dakarun sun jaddada cewa mashigar ruwa taHormuza rufe take, suna masu gargadin cewa duk wani jirgin da ya yi yunkurin wucewa zai fuskanci matakai masu tsauri.
Karin bayani: Iran ta gindaya sharadin wucewa ta mashigar Hormuz
Rahotanni sun nuna cewa a wannan Juma'a, an mayar da wasu manyan jiragen daukar kaya guda uku na kasashe daban-daban da suka yi kokarin wucewa ta mashigar Hormuz bayan sun samu gargadi daga rundunar ruwa ta Iran.
Tun bayan barkewar rikicin yankin, an takaita zirga-zirga a mashigar, duk da cewa ana barin wasu jiragen kasashe su rika wucewa.
A wani bangare kuma, kungiyar Houthi da ke Yemen ta ce a halin yanzu ba ta da shirin takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya, duk da hare-haren da ta taba kaiwa kan jiragen ruwa a baya.