Iran ta kai ga matakin kusa ga na karshe a yunƙurinta na sarrafa uranium
October 25, 2012Bisa ga dukkan alamu, ƙasar Iran ta cimma wani matsayi a matakinta na kaiwa ga sarrafa sinadarin uranium. Wannan kuma shi ne wani sakamakon binciken da ofisoshin wasu jakadan kasashen wajen suka ce sun samu. Wasu rahotanin sun bayana cewar a yanzu kam,kasar ta Iran ta samu kafa wasu na'urorin da suka rage mata gurin ci-gaba da sarrafa sinadarin wanda kasashen yammaci suka zargi ƙasar da yunkurin ƙera makaman nukleya zargin da hukumomin kasar suka yi watsi da shi. Kasar dai ta nace ne a kan duk wani yunkurin da ta yi a dangane da batu,na samarwa jama'an kasar wutar lantarki ne da kuma sha'anin kiyon lafiya. Kawo yanzu dai hukumar kulla da makamashi ta duniya bata ce komai ba akan wadanan sabbin bayanan wadanda kan iya haddasa gaugauta kaiwa kasar hari kamar yada Isra'ila ke barazana.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mohammad Nasiru Awal