1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kai karar Kanada gaban kotu ICJ

June 28, 2023

Iran ta kai karar Kanada gaban kotun duniya ta ICJ bisa zargin shigar mata hanci da kudundune ta hanyar bayyanata a matsayin kasar da ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

Hoto: eghtesadonline

Kasar Iran ta kalubalanci gwamnatin Ottawa da sanya sunanta cikin wadanda suka dauki nauyin 'yan ta'adda a shekarar 2012, a lokacin da Kanada ta yanke alakar diflomasiyya da kasar tare da rufe offishin jakadancinta da ke Tehran baya ga korar jami'an diflomasiyar Iran daga kasar.

Iran ta ce, Kanada ta take dokar kasa da kasa na hukuncin kotu da ya bai wa Iran umurnin mika wasu kadarori ga wadanda harin kungiyoyin da Tehran din ta dauki nauyi ya shafa. Sai dai har yanzu kasar Kanadar ba ta mayar da martani kan matakin na Iran ba.