1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kalubalanci matakin Amurka game da baki

June 7, 2025

Gwamnatin Iran ta yi Alla-wadai da matakin gwamnatin Shugaba Donlad Trump na sanya kasar cikin jerin kasashen da ta hana shiga Amurka. Shugaba Trump dai ya sanya kasashe 12 ne da ya haramta wa 'ya'yansu shiga kasar.

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Maxim Shemetov/REUTERS

Hukumomin na Iran dai sun bayyana abin da Amurkar ta yi, da wani nau'i na nuna dabi'ar wariyar launin fata.

A ranar Larabar makon jiya ne dai Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan dokar hana kasashe 12 shiga Amurka, yana mai kafa hujja da dalilai na tsaro.

'Yan kasashen da Amurkar ta hana shiga cikinta baya ga Iran din dai, su ne Afghanistan da Myanmar da Chadi da , Congo-Brazzaville da Equatorial Guinea da Eritrea da kasar Haiti da Libya da Somalia da Sudan da ma kasarYemen.

Akwai ma wasu kasashen bakwai da aka kakaba musu tasu dokar wadda ba ta kai wadannan tsauri ba.