1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta koma sufurin jiragen dakon mai a mashigin Hormuz

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 16, 2026

Jiragen ruwa biyar makare da fetur da kayan masarufi da abincin dabbobi sun ratsa ta tekun Indiya bayan ratsa Hormuz.

Yadda jigilar jiragen ruwa ke kasancewa a mashigin Hormuz ranar  14.06.2026.
Yadda jigilar jiragen ruwa ke kasancewa a mashigin Hormuz ranar 14.06.2026.Hoto: REUTERS

Iran ta sanar da komawa hada-hadar sufurin jiragen dakon manta ta ruwa, sa'o'i kalilan bayan cimma yarjejeniya da Washington, ta dakatar da yakin da suke gwabzawa na tsawon kusan watanni hudu.

Karin bayani:Iran na fuskantar tsangwama a gasar cin kofin duniya 

Gidan Talabijin na kasar ya rawaito cewa jiragen ruwa uku makare da man fetur, sun ratsa ta tekun arewacin Indiya, yayin da wasu biyu dauke da kayan masarufi da abincin dabbobi ke kan hanyarsu ta zuwa kudancin gabar ruwan, bayan wucewa ta mashigin Hormuz.

Karin bayani: Fata bayan yarjejeniyar Amurka da Iran?

Rahoton gidan talabijin din ya tabbatar da kawar da shingen dakarun Amurka daga mashigin Hormuz, domin ci gaba da jigilar makamashi da sauran hada-hadar kasuwanci ta mashigin, bayan dambarwar da aka sha, sanadiyyar yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan Iran a ranar 28 ga Fabarairun da ya gabata.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW