Iran ta musanta batun tattaunawa da Trump
September 26, 2019Talla
Shugaba Rouhani ya ce duk wata tattaunawa ba za ta yiwu ba muddin Amirka ta ci gaba da kafewa a matsayinta na kakaba takunkumai na kariyar tattalin arziki ga Iran, shugaban ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da jawabinbsa a zauren na Majalisar Dinkin Duniya.
Rahotanni sun ce matsayin da shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana, ya kara yin fatali da duk wani yunkurin da wasu manyan kasashen duniya suke da shi na sulhunta rikicin da ya kara daukar dimi tsakanin Amirka da Iran, tun bayan kaddamar da wani hari kan matatun man fetir din kasar Saudiyya a tsakiyar wannan watan, harin da kuma Saudiyya da Amirka suka nuna 'yar yatsa ga Iran da cewa ita ce ta ke da alhakin kai harin.