SiyasaAsiya
Iran: Dakarun juyin-juya hali ba 'yan ta'adda ba
February 2, 2026
Talla
A wannan Litinin kasar Iran ta gayyaci jakadun kasashen Turai da ke aiki a kasar, inda ta nuna rashin jin dadi da yadda aka saka sunan dakarun kare juyin-juya hali na kasar a matsayin 'yan ta'adda.
Wannan na zuwa lokacin da kasar Turkiyya take kokarin ganin ta shirya taro tsakanin kasar ta Iran da Amurka, domin warware sabanin da ke tsakanin kasashen musamman kan batun bunkasa makamashin nukiyar Iran. Tatataunwar idan ta samu nasara ta iya kawar da barazanar amfani da karfi da Amurka ke yi kan kasar ta Iran.
Tuni dai Amurka ta tura jirgin ruwan dakon jiragen saman yaki zuwa yankin ruwan na kusa da Iran, domin nuna cewa da gaskiya take yi, musamman kan batun na dakile bunkasa makamashin nukiliyar na Iran.