1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Iran ta nesanta kanta da zargin hallaka Donald Trump

November 9, 2024

Mahukunta a Tehran sun yi tir da alakanta su da yunkurin hallaka zababen shugaban kasar Amurka Donald Trump.

US-Präsidentschaftswahlen machen Schlagzeilen in iranischen Zeitungen
Hoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu/picture alliance

Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Iran a wata sanarwa da ta fidda a ranar Asabar ta ce ko kusa wannan zargin ba shi da tushe balle makama. 

Sanarwar ta kara da cewar Iran ba ta da hannu a yunkurin kisan jami'an Amurka na da ko ma na yanzu.

Duk wannan na zuwa ne bayan da a ranar Juma'a masu shigar da kara a Amurka su ka sanar da daukar mataki a kan wannan zargin.

Danganataka a tsakanin Amurka da Iran ta jima da yin tsami, inda ko a baya-bayan nan Amurka ta sake laftawa Iran din wasu karin takunkumai a kan abin da ta kira na taimakawa mayakan Hizbullah kai wa Isra'ila hari.

 

Karin Bayani: Isra'ila ta ce ta kammala harin ramuwar gayya kan Iran