1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Hukuncin kisa ga dillalen kwaya

Abdul-raheem Hassan
January 25, 2020

Kotu ta rataye mutumin mai shekaru 36 da mataimakinsa a tsakiyar gidan yarin da ke kudancin lardin Hormozgan, tare hukuncin zaman kurkuku ga sauran yaran gidansa.

Iran Todesstrafe
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Bolourian

Wata kotu a kasar Iran ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani shugaban masu safarar muggan kwayoyin maye da ya addabi yankin Gulf, kotun ta zargi mutumin da kisan gilla da fyade da fashi da makami da dillancin haramtattun kwayoyi.

Sama da shekaru biyar hukumomin da ke yaki da ta'ammali da kwayoyi a Iran ke tarkon mutumin da ya zama karfen kafa a yankin Gulf, an kwace ton na sinadarin nikotin 100 bayan kamashi a 2019.Sai dai Iran na shan suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama a kan yanke irin wannan hukunci.