1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta rataye wani da ta ce ya yi wa Isra'ila leken asiri

May 13, 2026

Iran ta kashe wani mutum da ta zarga da yi wa Isra’ila leken asiri, bayan kotu ta same shi da laifi tare da tabbatar da hukuncin kisa. Mahukuntan kasar sun ce ya bai wa Isra’ila bayanan sirri masu alaka da tsaron Iran.

Wani ke jami'in dan sandan Iran lokacin hukuncin kisa a bainar jama’a
Wani ke jami'in dan sandan Iran lokacin hukuncin kisa a bainar jama’a Hoto: Abedin Taherkenareh/EPA/picture-alliance/dpa

Iran ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mutum da ake zargi da yi wa Isra'ila leken asiri.

Rahotanni sun ce mutumin mai suna Ehsan Afreshteh ana zarginsa ne da bai wa hukumar leken asirin Isra'ila ta Mossad muhimman bayanai bayan samun horo a kasar Nepal.

Tun bayan barkewar rikici tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka, wannan ne mutum na shida da Iran ta kashe bisa zargin leken asiri.

Sai dai wata kungiyar kare hakkin bil Adama mai hedkwata a kasar Norway ta ce mutumin ya musanta zargin, tana mai cewa an tilasta masa amsa laifin ne a talabijin bayan tsare shi a killace.