1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta rufe cibiyar bunkasa harshen Jamusanci a Tehran

August 20, 2024

Jamus ta yi sammacin Jakadan Iran da ke a Berlin domin yi mata ba'asi kan rufe cibiyar bunkasa harshen Jamusanci a birnin Tehran, matakin da ya fusata hukumomin Jamus.

Ginin cibiyar bunkasa harshen Jamusanci a Tehran da Iran ta rufe
Ginin cibiyar bunkasa harshen Jamusanci a Tehran da Iran ta rufeHoto: dpa/picture alliance

Matakin na zuwa ne wata guda, da rufe cibiyar bunkasa addinin Islama ta birnin Hamburg na Jamus da ake alakan shi da Iran, kamar yadda jaridar Mizan ta wallafa a shafinta na internet. Tehran ta ce ana amfani da cibiyar wajen gudanar da ayyukan da ba su dace ba, da ake ci gaba da bincike a kai; ciki har da hada-hadar kudade ta haramtacciyar hanya.

Karin bayani: Jamus ta ce Iran ta tallafa dakile rikicin Gabas ta Tsakiya

A sanarwar da ma'aikatar kula da harkokin wajen Jamus ta fitar, ta bukaci gwamnatin Iran da ta gaggauta bude cibiyar domin ci gaba da gudanar da karatu. An dai kafa cibiyar ne a shekarar 1995 domin bunkasa koyar da hashen Jamusanci da kuma samun gurabe da damarmaki na Jamus ga al'umma a Iran.